Illolin kallon hotuna ko fina-finan Batsa


Hotunan bidiyo na batsa, hotuna ne masu
motsi da suke da shafuka daban-daban a
intanet a wannan zamanin. Kafin shaharar
intanet a duniya, masu irin wannan ta’asa
sukan yi amfani ne da kaset na bidiyo
wurin yada badalar tasu, amma samuwar
intanet sai suka samu ci gaban mai hakar
rijiya. Galibi an fi ganin matasa su ke da
kaso mafi yawa da ke kallon bidiyo na
batsa, duk da cewa akwai sauran rukunin
jama’a a matakai daban-daban da su ma
za a iya samun su dumu-dumu suna kallo.
Masu wannan halin anya kuwa kun san
illolin haka? – Shin kun san abubuwan da
kuke kallo yana daga cikin manyan laifuka
(kaba’ir ). – Shin kun san abin da kuke
kallo yana gadar da kaskanci da kuma
rauni ta kowane bangare. – Shin kun san
abin da kuke kallo yana kawo raunin idanu
da kwakwalwa da yawan mantuwa, abu
kankani sai kamanta. – Shin kun san
wannan kallon yana sa mutuncin mutum
ya fadi a idon Allah. – Shin kun san
wannan kallon yana hana mutum samun
ilimi ko mantashi. – Shin kun san wannan
kallon yana hana ka /ki samun jin dadin
rayuwar aure mai inganci da mijinki ko
matarka, kuma duk da kuna son juna. –
Shin kun san cewa za ku iya mutuwa a
cikin wannan yanayin (mummunar
cikawa). – Shin kun san jikinku zai gaya
muku ko badade ko bajima in baku tuba
ba. -Shin kun san duk abin da kuka yada
kuna da zunubi, imma ya yi sanadiyyar
lalacewar wani kuna da zunubin ko da
kuna kwance a kabari har izuwa kiyama. –
Shin kun san cewa duk wanda yabar wani
abu domin Allah, Allah zai musanya masa
da abin da ya fishi alkairi. – Shin kun san
cewa Allah yana farin ciki sosai da tuban
bawansa. – Shin kun san cewa Allah zai
wadata ku da falalarsa idan kuka kame
kawunanku daga aikata haramun. – Shin
kun san cewa sha’awar ‘yan mintina ta
haramun tana dai-dai da azabar shekaru.
‘Yan uwa musulmai ku taimaki ‘yan
uwammu wajen isar musu da sakon nan
ko allah zai shirya su ta dalilin ku sai ku
samu lada.
Allah ya ganar damu

Post a Comment

0 Comments