Falalar Azumin Watan Ramadan

Azumin Ramadan yanada falaloli da yawa.
Daga cikin falalar azumin sun hada da:-
1. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda
yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace:
Manzon Allah {S.A.W} yace:
"Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko
makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna
kankaresu (Bukhari).
2. Yazo a hadisai da dama cewa:
Dukkan aikin Dan Adam nasane Malaikune suke
rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi
Yake sakawa wanda yayi shi (hadisin ya tabbata
acikin targhib wattarhib, juz'I na farko shafi na
75).
3. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan
Abdullahi (R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.}
cewar:
Azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa
dashi daga wuta.
3. Sannan hadisi ya tabbata daga Mu'azu dan
Jabal (R.A.) cewa:
Hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin
bazan nuna maka kofofin alheriba ?
Sai yace na'am ya Rasulullah.
Sai yace azumi garkuwane.
4. Sannan akwai hadisin Abi Umamata (R.A.)
yace:
"Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da
wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai
yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa"
(dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib,
tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na
578).
6. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah.
7. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin
Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama
sannan a daure shaidanu kamar yadda ya
tabbata a hadisin Abi Huraira.
(Kuduba Sahihul Bukhari 1899).
8. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya
ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace:
"Warin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da
turaren Al-miski a wurin Allah.
Hadisine sahihi.
9. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin
Sa'ad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace:
Acikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta
Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin
kiyama, babu wanda zai shigeta sai su.
Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake
shiga
(Kuduba Sahihul Bukhari 1896).
Tirmizi yakara bayani a cikin riwayarsa cewar
wanda ya shigeta bazaiji kishin ruwaba (Qishirwa
ba) har abada. Allah ya Albarka ci rayuwar mu
ya
mana jagoranci yasa albarka a cikin karatun mu
yasa
sauki a ciki yasa muna daga cikin bayin da zaa
yanta a
wannan wata mai Albarka

Post a Comment

0 Comments