Hausa novels Dai Wasu Qagaggun Labarai ne da ake Kirkirarsu domin fadakarwa, Ilmantarwa, Nishadantarwa, wa'azantarwa wani lokacin kuma domin Koyar da wani Darasi na Rayuwa.

  Mafi Yawan Wadannan Novels da ake Rubutawa akan Rubutasu ne Akan Labarin Soyayya me cike da Farin ciki, Jin Dadi, Kwanciyar hankali da kuma Daula.

 Kuma a cikin wadannan Littattafai na HAUSA NOVELS Idan Marubuci ko marubuciya zasu bada Misalin Saurayi Sukan Zuzutashi, su riqa Kodashi, Suna bayar da misalin kamannin Shi ta yadda idan a filine ba tayadda za'a iya samun irin wannan Zuqeqen Saurayi cikin Sauqi.
Misali, Mu kalli kamannin wannan Saurayi :
"Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau" domin Allah Ina Za'a sami irin wagga saurayi a wannnan lokaci ?

To idan Ya kasance Mace musamman Budurwa Ta Lazimci karanta Ko kuma Sauraron wadannan Littattafai na HAUSA NOVELS sai ta riqa ji A zuciyarta tana Son Ace mijin da Zata Aura ya Kasance kamar irin wanda take karanta kamanninsa a Cikin Littafi, To da zaran Hakan Yayi Tasiri a Zuciyarta shikenan Duk Saurayin Da yazo wajenta ko yace yana Sonta sai taga ai baima Yi Rabin na Novel ba, Sai ta Rabu dashi.

A haka a haka, Kullum Tana Sauraron ta inda Saurayi Irin na Hausa Novels zai Bullo sai kuga Ta dade A gidansu ba tayi Aure ba, Kuma Abun Yazo Yana damunta da Iyayenta, ALLAH YA KYAUTA.

IDAN KIN KASANCE KINA DAYA DAGA CIKIN MASU SAURARON MIJI IRIN NA NOVELS TO INA MAI BAKI SHAWARA da kisani Cewar Shi Hausa novel bawai duk Labaran da suke a ciki bane Gaskiya, a'a Qagarsu akai Akayi musu Kwalliya da Kalamai suka zamo Kamar Gaske.

 Ba Zai yiwu ace kin Auri Miji irin Wanda kike karantawa a novels ba. Kawai dai Ki nemi Zabin Allah.
Allah Ya hadamu da Abokan Rayuwa naGari 🙏
                       ✍️ USTAZ KHAN ✍️