Shawarwari 5 da zasu amfani ko wacce mace





  Assalamu Alaikum, ina Maki Barka da zuwa Wannan Shafi. Ina Rokon Allah da ya sanya wannan Rubutu nawa ya amfani duk wadda ta karanta shi 🙏


  To Amarya shi dai Aure Kamar yadda Kika Sani Ibada ne Kuma bautar Ubangiji ne, Saboda Haka Ba Abin Wasa bane.


  Wadannan wasu Nasihohi ne Guda Biyar waɗanda Na rubuta su domin amfanin yan uwa mata.


                           Ga sunan :-


• LADABI DA BIYAYYA : 


 Yake yar Uwata Kisani Wajibinki ne ki yiwa mijinki Biyayya, Yi nayi, Bari na Bari, Dole Kibi Dukkan Umarninshi Matukar bai Sabawa Shari'ar Musulunci ba, Domin Aljannarki Tana Karkashin Kafar shi.


• KI ZAMO MAI TSAFTA : 


 Ki sani ita Tsafta Abace Da Take Da Matukar Muhimmanci a zaman Aure, Domin Babu wani Namiji Da zaiso ace matarsa ta kasance Marar Tsafta.


  Kuma Ita Tsafta Tana Kara Matsayi da kuma Dankon Soyayya a Zuciyar Miji, Saboda Haka nake yi miki Nasiha Yake Yar Uwata Komin tsufanki Tofa Ki Zamo Mai Tsafta da Iya Tsara Kwalliya, Bawai Sai Zakije Anguwa ba.


• KI ZAMO MAI TAUSAYAWA GA MIJINKI :


  Ki Tausayawa Mijinki, Idan Ya shiga Wani Hali ki Taimaka masa, Hakan Zaisa Ki Zamo Tauraruwa mafi Haske A Cikin Zuciyarsa.


• KI KULA DA MIJINKI :  


 Abinda yayi karanci kenan A wannan Zamani namu, Shi Yasa Yawancin Maza Sai Suyi ta Aure-Aure Ba kan gado, Yake Yar Uwata Ki zamo mai Tsananin Nuna Kulawa ga mijinki; Idan Zai fita Kiyi masa Rakiya Sanna Kiyi masa Addu'ar samun nasara da kuma Kariya,


Idan ya dawo kuwa ki tarboshi, ki kawo masa ruwa mai sanya ko kuma abinda kika ga yana da bukata, Koda ace mijinki Tsohone Ki bashi Kulawa Yadda Ya kamata don Ba wanda yaki kulawa.


• KI RIKE SIRRIN MIJINKI : 


 Kada Ki sake kiyi Kuskuren yada sirrin mijinki, Koda A cikin Yan Uwanki ne Ko kuma Kawayenki Koma dai a ina ne, Domin Kuwa Koda kin nuna masa Kulawar, Soyayya, Tausayawa, Komin Tsaftarki Indai Kika Kasa Rike Sirrin Mijinki Tofa Kin Tashi a Tutar Babu. Babu wani Namiji da zai iya zama dake alhali ba zaki iya rike sirrin Shi ba.


  Kada Ki Bayyana sirrin Mijinki Koda Ga Iyayen ki ne domin Hakan Ba karamin Ganganci bane.


  WASSALAMU ALAIKUM.


Daure ki gayyato Yan uwa Zuwa Wannan Shafi Domin Suma Su Amfana 🙏



Post a Comment

0 Comments