Abubuwan Dake Faruwa Ga Jikin Me yin AZUMI

A kowacce shekara miliyoyin musulmai suna azumi tun daga
fitowar rana har faduwarta, na tsawon kwanaki 20 ko 30 a
cikin watan Ramadan.
A shekarun baya-bayan nan dai Ramadan na fadowa ne a
watannin bazara a kusurwar duniya daga arewa, hakan zai
janyo ranaku masu tsawo da kuma yanayi mai dumi.
Hakan na nufin cewa wasu kasashe kamar su Norway, mutane
za su yi azumi na tsawon sa'o'i 20 a wannan shekarar.

Shin yin azumi zai iya yi wa jikin mutum illa?
Ga abin da ke
faruwa da jikinku idan kuka yi azumi na tsawon kwanaki 30.
Ramadan: Tsawon azumi a kasashen duniya
Ramadan 2019: Musulmi sun fara azumi
Lokaci mafi wuya - kwanaki biyu na farkon
azumi
A ka'ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai
an shafe sa'a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci.
Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da
abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin.
Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin
da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi.
Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai
koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi.
Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa
wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum
ya kamu da ciwon siga.
Amma, raguwar yawan sikarin da ke jikin mutum zai iya janyo
kasala da rashin karfi.
Za ku iya fuskantar ciwon kai, da jiri, har ma da tashin zuciya
da warin baki.
A wannan lokacin ne mutum ke fuskantar tsananin yunwa.
Hattara da rashin ruwa a jiki - Rana ta 3 zuwa
ta 7
A lokacin da jikin mutum ya fara sabawa da azumi, kitse na
raguwa kuma shi ne ke zama sikari a jini.
Dole sai an mayar da ruwan da mutum duk ke rasawa a yayin
azumi, in ba haka ba zufa za ta iya janyo rashin ruwa a jiki.
Dole ne abincin da mutum zai ci ya kasance masu gina jiki da
masu kitse.
Yana da muhimmanci mutum ya samu abinci mai gina jiki,
wanda ke da gishiri da ruwa.
Sabawa da azumi a yanzu - Rana ta 8 zuwa ta
15
A mataki na uku, ya kamata mutum ya fara ganin sauyi a
yanayinsa a yayin da jiki ya fara sabawa da azumin.
Dr Razeen Mahroof, wani kwarare kan maganin da ke kashe
ciwo da bangaren kulawa ta musamman a asibitin
Addenbrooke's da ke Cambridge, ya ce baya ga haka azumi na
da amfani daban-daban.
''A rayuwar mu ta yau da kullum ba kasaifai ake cin nau'ikan
abinci daban-daban ba, kuma hakan na hana jiki gudanar da
ayyukansa yadda ya kamata''
''Ana gyaran hakan a lokacin azumi, yana karkatar da jiki ya yi
aikinsa da ya kamata.''
Azumi na taimakawa jiki wajen samun sauki cikin gaggawa da
kuma hana jiki yaki da cututtuka.
Tsaftace ciki - Rana ta 16 zuwa ta 30
Idan aka ci rabin watan Ramadan, jikin mutum yana sabawa
da azumi.
Hanji da koda da huhu da ma fatar mutum na tsaftace kansu.
''A wannan mataki, wadanan sassa na jiki sun dawo da aiki
yadda ya kamata. Kwakwalwar mutum da hankalinsa na
sauyawa kuma ana samu karin kuzari,'' in ji Dokta Mahroof.
''Jikin mutum na kasa samun karfi. Wannan shi ne lokacin da
yake shiga cikin 'yunwa' kuma ya kan samu kuzari. Hakan na
faruwa ne idan mutum ya tsawaita azumi zuwa kwanaki da
makonni.''
''Ayayin da ake azumtar Ramadan daga fitowar alfijir zuwa
faduwar rana, muna da damar tsara jiki ya samu abinci mai
gina jiki da wadataccen ruwa. Hakan na gyara jiki da kuma
taimakawa wajen rage kiba.''
Shin azumi na taimakawa Lafiyarmu?
Dokta Mahroof ya ce eh, sai dai ya gindaya sharudda.
''Azumi na da kyau ga lafiyarmu saboda yana taimakawa wajen
mayar da hankali kan abin da za mu ci da kuma lokacin cin su.
Sai dai kuma, duk da cewa babu matsala idan mutum ya shafe
wata yana azumi, ba shawara ba ce a kuma zarce da azumin
ba.''
''Ci gaba da azumi ba hanya mai kyau ba ce na samun raguwar
kiba na tsawon lokaci saboda sannu a hankali jikinka zai daina
narkar da kitse don kara ma kuzari, kuma za ka tara kwanji.
Hakan matsala ce ga lafiya domin yana nufin jikinka ya shiga
yanayi na yunwa'.''
Likitan ya shawarci cewa ban da watan Ramadan akwai
lokutan da mutum ka iya ware a sauran watanni ko mu ce
kwanaki a cikin sati da mutum zai iya azumi - misali sau biyu a
sati - hakan ya fi taimakawa lafiya.
''Azumin Ramadan, na taimakawa jiki ya daidaita kansa, hakan
na iya nufin rage kiba da narkewar kitse marasa amfani.''

Post a Comment

0 Comments